Nijar

Nijar ta ba ‘Yan Boko Haram wa’adin tuba

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou France 24

Gwamnatin Nijar ta ba ‘yan Kungiyar Boko Haram zuwa 31 ga watan Disemba su mika wuya, kuma duk wanda ya bari wa’adin ya cika ba za a amince da tubar shi ba.

Talla

Gwamnan Jihar Diffa ne yankin da ke fama da rikicin Boko Haram ya sanar da matakin, lokacin wata ziyara a wani sansanin da ake karbar ‘yan Boko Haram da suka tuba a garin Douduoumaria.

Mahamadou Laoualy Dan Dano ya ce bakin alkalami zai bushe ga duk dan Boko Haram da ya bari wa’adin ya cika.

“Duk wanda bai tuba ba har bayan 31 ga Disemba to sai dai ya san makomarsa”, a cewar Gwamnan na Diffa Mahamadou Laoualy Dan Dano.

Tun a karshen watan Disemban bara ne Nijar ta mika hannun karbar tubar ‘yan Boko Haram inda wasunsu da dama suka mika wuya.

A cewar Gwamnan Diffa har yanzu kofar tuba a bude ta ke ga ‘Yan Boko Haram har zuwa 31 ga Disemba.

Shirin karbar tubar na Nijar ya shafi kula da rayuwar ‘yan Boko Haram da suka tuba ta hanyar gyara hali da kuma samar ma su makoma mai kyau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.