Najeriya

‘Yan Boko Haram sun kai hari sansanin sojin Najeriya a Marte

Dakarun Najeriya da ke fada da Boko haram Boko Haram.
Dakarun Najeriya da ke fada da Boko haram Boko Haram. AFP PHOTO/REINNIER KAZE

'Yan kungiyar Boko Haram sun kai hari a wani sansanin soja a yankin arewa maso gabashin Najeriya, inda suka kashe soja guda kuma suka jikkata wasu tara tare da kwasar ganimar makamai.

Talla

Mayakan sun kai harin ne a ranar Juma’a a sansanin sojin Najeriya da ke garin Marte, kamar yadda wani jami’in tsaro ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa AFP wanda ya nemi a sakaya sunansa.

Majiyar ta ce mayakan sun kwashi makamai da albarussai da dama da motoci.

Majiyar ta kara da cewa ‘yan ta’addar sun fi yawan sojojin da suka riska a sansanin, lamarin da ya sa sojojin suka arce bayan sun shafe lokaci suna musayar wuta.

Zuwa yanzu dai babu wani bayani daga rundunar sojin Najeriya game da harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.