Afrika

Afrika ta samu wakilcin kasashe 4 a hukumar kare hakkin dan adam

Zauren Hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya da ke Geneva.
Zauren Hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya da ke Geneva. REUTERS/Denis Balibouse

Najeriya, Angola, Senegal da Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, na daga cikin kasashe 15 da aka zaba domin zama wakilai a Hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya mai wakilai 47.

Talla

Sauran kasashen da aka zaba sun hada da Australia, Afghanistan, Qatar, Pakistan da kuma Chile.

Sai dai Amurka ta bayyana bacin rai kan zaben da aka yi wa Jamhiriyar Congo saboda tashin hankalin da ake samu a kasar, da kuma binciken da yanzu haka Majalisar ke yi akan sojin kasar, dangane hallaka fararen hula.

Kan haka ne Jakadiyar Amurka a Majalisar Nikky Haley, ta ce Majalisar Dinkin Duniyar na neman a yi mata garambawul ganin yadda aka zabi kasar ta Jamhuriyar Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.