Isa ga babban shafi
Nijar

Gwamnatin Nijar za ta saye abincin da aka noma

Gwamnatin Nijar za ta saye abincin ne da nufin adanawa domin hana ‘yan kacare wawushe amfanin gonar a wulakance.
Gwamnatin Nijar za ta saye abincin ne da nufin adanawa domin hana ‘yan kacare wawushe amfanin gonar a wulakance. AFP/Issouf Sanogo
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
1 Minti

Gwamnatin Nijar ta ware kudi Cefa biliyan 24 don sayen cimaka daga hannun manoman karkara a fadin kasar, da nufin hana ‘yan kacare wawushe amfanin gonar a wulakance.

Talla

Kimanin ton dubu dari na abincin da aka noma ne gwamnatin za ta saye da suka kunshi hatsi ton dubu hamsin, dawa ton dubu 25 masara ton dubu 15 da kuma shinkafa ton dubu 10.

Ministan kasuwanci na kasa Sadu Saidu ne ya jagoranci bikin kaddamar da soma sayen abincin a kasuwar garin Sabon Mashi na yankin Dakwaro a Jihar Maradi.

Gwamnatin na son maida rumbunta na tsimi ne da nufin taimakawa manoma a lokacin tsakanin rani da abincin ke wahala da tsada kuma ofishin OPVN ne aka bai wa umurnin sayen abinci a kasuwannin cimaka a yankuna daban-daban.

Farashin da gwamnatin ke sayen amfanin gonar ya banbanta tsakanin jihohin kasar.

A Maradi farashin gwamnati na tashi ne jika sha bakwai buhu mai cin kilogram dari, yayin da ‘yan kacare ke saya akan jika sha takwas abin da ke sa suke kin sayar wa bangaren gwamnatin duk da jan hankalin da ake musu.

A Agadez manoman kan sayar akan jika 25 yayin da a Tahoua gwamnati ke saya akan jika 22 kasancewarsu yankuna ne da ba a noman hatsin sosai.

Manoman sun bukaci gwamnati ta hada da wake wanda aka noma sosai a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.