Kenya

Hukumar zaben Kenya na shakkun gudanar da zabe

A wani taron manema labarai da Wafula Chebukati ya kira yau Laraba 18 ga watan Oktoba ya sanar da cewa yanzu haka hukumar bata da tabbacin yiwuwar zaben bisa gaskiya da amana.
A wani taron manema labarai da Wafula Chebukati ya kira yau Laraba 18 ga watan Oktoba ya sanar da cewa yanzu haka hukumar bata da tabbacin yiwuwar zaben bisa gaskiya da amana. REUTERS/Thomas Mukoya

Hukumar zaben Kenya ta nuna shakku kan yiwuwar gudanar da sahihin zabe a babban zaben da ake shirin yi cikin mako mai zuwa. A cewar hukumar babban kalubalen da zaben ke fuskanta ya kunshi katsalandan daga bangaren manyan Jam'iyyun siyasa baya ga rarrabuwan kai na cikin gida. 

Talla

Shugaban hukumar zaben Kenya Wafula Chebukati wanda ke sanar da hakan lokacin da wata kwamishinar zabe Mrs Akombe ta ajiye aikinta tare da yin gudun hijira zuwa birnin New York na Amurka kan abin da ta kira barazana ga rayuwarta,saboda abun data kira barazana ga rayuwarta.

Chebukati ya yi gargadin cewa babu tabbacin samun zabe mai inganci a halain da ake ciki, inda ya bukaci shugabannin siyasa su daina katsalandan da shisshigi a harkokin hukumar.

A cewarsa, kafin yanzu hukumar ta shirya tsaf don gudanar da sahihin zabe, amma a yanzu hukumar na cike da shakkun iya gudanar da zaben yadda ya kamata.

Tun da farko dai an sanar da sake zaben ne baya da kotun kolin kasar ta rushe zaben farko na ranar 8 ga Agusta da ya bai wa shugaba mai mulki Uhuru Kenyatta rinjaye kan abokin karawarsa Raila Odinga sakamakon da Odinga ya yi watsi da shi.

Sai dai kuma bayan sanya ranar 26 ga watan Satumba a matsayin ranar da za a sake gudanar da zaben, daga bisani Jagoran adawa Raila Odinga ya sanar da janyewa daga zaben kan abin da ya kira da rashin cika wasu sharudda daya gindaya tun da farko, lamarin da ya kara rura wutar rikicin siyasa a kasar ta Kenya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.