Bakonmu a Yau

Shugaban NLC Ayuba Waba, kan rashin biyan albashin ma’aikata a Jihohi

Sauti 03:38
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari The U.S. | Post-Nigeria

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana damuwarsa da yadda wasu Gwamnonin Jihohi ke kin biyan albashin ma’aikata, matakin da ya jefa ma’aikatan cikin halin kakanikayi. Yayin da ya ke ganawa da tawagar Gwamnonin a ofishinsa, shugaban ya ce yana mamakin yadda Gwamnonin ke iya bacci alhali suna sane da hakkin ma’aikatansu. Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Ayuba Waba, shugaban kungiyar kwadago a Najeriya.