Afrika ta tsakiya

Yunwa na ajalin yara a Afrika ta tsakiya

Rikicin kabilanci da siyasa ya jefa al'ummar Afrika ta tsakiya cikin mawuyacin hali
Rikicin kabilanci da siyasa ya jefa al'ummar Afrika ta tsakiya cikin mawuyacin hali RFI / Olivier Rogez

Ofishin Jinkai na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa yunwa na ci gaba da hallaka yara kanana a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya saboda yadda tashin hankali ya tilastawa jami’an aikin agaji tserewa daga kasar.

Talla

Jami’in Majalisar Dinkin Duniya Najat Rocchdi, ya ce sakamakon ficewar jami’an agajin yanzu haka ya sa ba a samun kayan agajin da ake tallafawa yaran, abinda ke taimakawa wajen rasa rayukansu.

Rashin kudi ya sa an rage abincin da ake taimakawa ‘yan gudun hijira daga abinda aka saba ba su.

Akalla mutane 600,000 aka raba da gidajen su bayan wasu 500,000 da suka gudu suka bar kasar.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci kwamitin Sulhu da ya amince da tura karin dakarun samar da zaman lafiya 900 zuwa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya domin kaucewa barazanar tsaron da ake fama da shi yanzu haka.

Yayin gabatar da rahoto kan halin da ake ciki, Guterres ya ce Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya na bukatar karin dakaru domin tallafawa 12,000 da yanzu haka ke aikin samar da tsaro.

Sakataren ya ce tun bara harkokin tsaro na ci gaba da tabarbarewa a Bangui, saboda haka yana bukatar Karin sojoji 900 domin tallafawa wadanda ke kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.