Togo

An hallaka masu zanga-zanga 4 a Togo

Hoton bidiyon da ke nuna wasu daga cikin masu zanga-zanga a birnin Lome yayinda ake kone tayoyi. Ranar 18, ga Oktoba 2017.
Hoton bidiyon da ke nuna wasu daga cikin masu zanga-zanga a birnin Lome yayinda ake kone tayoyi. Ranar 18, ga Oktoba 2017. REUTERS/via Reuters TV

Gwamnatin kasar Togo ta tabbatar da mutuwar mutane 4 a arangamar da suka yi tsakanin masu zanga zanga dake adawa da ci gaba da mulkin iyalan gidan Gnassingbe da kuma jami’an tsaro.

Talla

Gamayyar jam’iyyun adawar kasar sun yi watsi da haramcin gudanar da zanga-zangar da gwamnati ta kafa, wanda ta ce ta dauki matakin ne don tabbatar da tsaron dukiya da kuma rayukan ‘yan kasar, dalilin kenan da ya sanya jami’an tsaro amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga zangar.

Kanal Yark Damehame ministan tsaron kasar ya shaidawa manema labarai cewa, abu ne mawuyaci a tantance wanda yayi harbin kan masu zanga zangar, kasancewar kowane bangare na jami’an tsaron da dandazon ‘yan adawar na dauki da makamai.

Zuwa yanzu akalla 'yan adawa 60 ‘yan sandan kasar ta Togo suka tsare, wadanda suka kame yayinda suke gudanar da zanga-zangar.

Rahotanni sun ce rikicin baya bayan nan ya biyo bayan kama wani limamin juma’a da ake zargi da kira ga magoya bayan sa da su kai hari kan jami’an tsaron da suka tinkare su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.