Kamaru

"Mutanen yankin Inglishi na iya daukar makamai a Kamaru"

Garin Bamenda na cikin yankin Ingilishi a Kamaru da ake zanga-zanga
Garin Bamenda na cikin yankin Ingilishi a Kamaru da ake zanga-zanga REUTERS/via Reuters TV

Kungiyar International Crisis Group da ke nazari kan rikice rikice a duniya ta ce abu ne mai yiyuwa mazauna yankunan da ke magana da Turancin Ingilishi a kasar Kamaru su fara yin amfani da makamai a gwagwarmayar da suke yi.

Talla

A cikin rahoton da kungiyar ta fitar, ta bukaci Paul Biya ya yi amfani da matsayinsa na shugaba domin shiga tattaunawa da mazauna yankin da nufin kwantar da hankula.

ICG ta ce har yanzu ana zaman dar dar a yankin na Kamaru duk da gwamnati ta tura tawaga da ta kunshi Firaminista Philemon Yang domin tuntuba da kuma tattaunawa da shugabannin yankin masu magana da ingilishi a kudu masu yammacin kasar.

Tuni dai gwamnatin Kamaru ta haramta gudanar da duk wani gangami musamman bayan babbar Jam’iyyar adawa ta SDF ta sanar da shirya gangami a ranar Asabar a Douala domin nuna goyon baya ga mutanen yankin masu magana da Ingilishi.

Akalla mutane 40 suka mutu cikin kwanaki 4 a rikicin yankin bayan a ranar 1 ga watan oktoba mutanen yankin na Ingilishi sun ayyana samun ‘yanci.

Rahoton ICG ya ce mutane da dama ne suka mutu a ranar 1 ga Oktoba sannan tsakanin 28 zuwa 2 ga Oktoba mutane 40 suka mutu yayin da sama da 100 suka jikkata.

Tun a watan Nuwamban 2016 ne mutanen yankin da ke magana da Ingilishi suka kaddamar da zanga-zanga kan yadda gwamnatin Yaoundé ta maida su saniyar ware.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.