Nijar-Chadi

Nijar ta tabbatar da ficewar Sojojin Chadi a Diffa

Sojawan Nijar za su ci gaba da tafiyar da tsaro a yankin Diffa bayan ficewar dakarun Chadi
Sojawan Nijar za su ci gaba da tafiyar da tsaro a yankin Diffa bayan ficewar dakarun Chadi REUTERS/Stringer

Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun tabbatar da ficewar sojojin Chadi da ke yaki da kungiyar Boko Haram a Yankin Diffa, tare da cewa sun janye ne kada kadan a watanni shida.

Talla

Barkai Issofou, ministan da ke kula da huldar jama’a ya tababtar da haka a gaban ‘Yan Majalisun kasar wadanda suka sake tsawaita dokar ta bacin da aka kafa a Yankin.

Ministan ya ce yanzu haka sojojin Nijar sun maye gurbin na Chadi domin samar da tsaro a Jihar ta Diffa.

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou ne ya nemi taimakon Chadi domin yakar Boko Haram bayan harin da ‘yan ta’addar suka kai a yankin Bosso inda mutane 26 suka mutu da suka hada da Sojojin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.