Togo

Shugabannin yankin yammacin Afrika na kokarin yayyafa ruwa, a watura siyasar Togo

Wata hanyar birnin Lome inda masu zanga zanga su ka yi dauki ba dadi da yan sanda.18 oktoba 2017. Image tirée d'une vidéo.
Wata hanyar birnin Lome inda masu zanga zanga su ka yi dauki ba dadi da yan sanda.18 oktoba 2017. Image tirée d'une vidéo. ©REUTERS/via Reuters TV

Daya daga cikin manyan masu nuna adawa ga shugaban Faure Gnassingbe na Togo, Tikpi Atchadam ta kafar Radiyo france internationale (RFI) Ya yi kira ga shugaban Faransa Emmanuel Macron da ya yi kokarin shiga tsakani wajen samar da mafita ga rikicin siyasar kasar ta Togo, da aka kwashe watanni 2 ana tafkawa tsakanin gwamnati da yan adawa.

Talla

Tun karshen watan ogusan wannan shekara ne, yan adawa suka kara rubanya zanga zangoginsu wajen son tilastawa shugaban kasar Faure Gnassingbe ya yi murabus daga kan mulkin kasar da zura’ar gidansu ta kwashe sama da shekaru 50 tana.

Ita dai wannan zanga zangar kin jinin mulkin zuri’ar Iyadema da yan adawar ke yi, ta rikide ya zuwa mummunan tashe-tashen hankulla ne, da suka yi sanadiyar mutuwar sama da mutane sama da 10 a watanni 2 da suka gabata.

A firarasa da RFI shugaban jam’iyar Adawar ta PNP da ya yi kaurin sunan wajen nuna adawa ga shugaba Faure Gnassigbe, Mr Tikpi Atchadam ya ce shuwagabannin yankin da dama sun yi ta yin kokarin shiga tsakani wajen shawo kan shugaba Faure Gnassigbe ya sauka kan mulki amma ya ki.

Shugaban Guine Alpha Konde mai rike da shugabancin kungiyar tarayyar Afrika na daya daga cikin wadanda ke ta kokarin ganin bangarorin 2 sun fahimci juna amma abin ya ci tura ,

Shugaba Alassan Watara ta Cote d’Ivoire ya tura tawaga a Lome domin yayyafa ruwa ga wutar rikicin.

A ranar Alhamis sojoji sun buda wuta kan masu zanga zanga, inda suka kashe uku, tare da jikkata wasu da dama.

Sannu a hankali dai za a iya cewa rikicin siyasar kasar ta Togo na daukar mummunar hanya lura da irin makamanciyar wannan zanga zanga ta kai wasu kasashe a cikin halin ni iyasu a nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.