Zimbabwe

Girmama Mugabe daga hukumar lafiya ya haifar da damuwa

Robert Mugabe,Shugaban kasar Zimbabwe
Robert Mugabe,Shugaban kasar Zimbabwe SEBASTIEN RIEUSSEC / AFP

Kungiyoyi masu zaman kan su a Zimbabwe da kasar Amurka na ci gaba da nuna damuwa bayan da kungiyar lafiya ta duniya WHO ko OMS ta nada Shugaba kasar Zimbabwe jakadan ta na musaman ga ayyukan jinkai.

Talla

Shugaba Mugabe na fuskantar takunkumi daga hukumomin Amurka bisa laifin keta hakkokin bil adama, tareda aikata laifukan da ake dangatawa da kisa.

Daga Sakatary harakokin wajen Amurka ,wannan lambar da aka baiwa Mugabe mai shekaru 93 a Duniya ya sabawa duk wasu ka’idojin tafiyar da ayyuka na hukumar lafiya ta Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.