Najeriya

Dambarwa dangane da dawowar Maina a aikin gwamnati

Tambarin hukumar yaki da rashawa a Najeriya EFCC.
Tambarin hukumar yaki da rashawa a Najeriya EFCC. RFI / Pierre Moussart

Hukumar EFCC da ke yaki da rashawa a Najeriya sun ce yanzu suna bukatar yin bincike a kan tsohon shugaban kwamitin yi wa tsarin fansho gyara Abdulrasheed Maina.

Talla

An tube Maina daga aikin gwamnati a shekara ta 2013 saboda samun sa da zargin aikata ba daidai ba, yayin da hukumar EFCC ta fara bincikensa da rashawa a shekara ta 2015.

To sai dai bayanai na nuni da cewa an sake dawo da tsohon shugaban kwamitin na gyaran tsarin biynan fansho a cikin aikin gwamnati har ma da yi ma sa karin girma.

Ma’aikatan cikin gida ta Najeriya ta ce ofishin shugaban ma’aikata ne ya dawo da wanda ake zargin a kan aikinsa tare da nada shi a matsayin shugaban sashen kula da ma’aikata baki na baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.