Nijar-Amurka

Majalisar Amurka ta nemi sanin dalilin shigar sojin kasar yaki a Nijar

Sojin Nijar na sintiri a yankin Ayorou kusa da iyakar kasar da Mali
Sojin Nijar na sintiri a yankin Ayorou kusa da iyakar kasar da Mali © ISSOUF SANOGO / AFP

Yanzu haka majalisar dattawan Amurka ta fara bincike dangane da dalilan tura sojojin kasar zuwa Nijar, inda hudu daga cikinsu suka rasa rayukansu sakamakon harin ba zata da aka kai ma su kusa da iyakar Nija da Mali.

Talla

Sanata John McCain ya gana da sakataten tsaron Amurka Jim Mattis dangane da wannan batu, inda ya nemi karin haske da farko dangane da dalilan shigar Amurka a fagen daga da kuma yiyuwar sakaci har aka kashe hudu daga cikinsu a wannan hari da aka kai ranar 4 ga watan okotban 2017.

Wasu bayanai na cewa tuni aka cafke dagacin garin Tongo-Tongon inda lamarin ya faru, bisa zargin cewa shi ne yana da alaka da maharan, yayin da wasu bayanai ke cewa dagacin, ya jinkirta kawo karshen wani taro da aka yi tsakanin ayarin sojojin Nijar, na Amurka da kuma shugabannin al’umma a yankin nashi, ga alama domin bai wa maharan damar kai hari akan jami’an tsaron.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI