Sahel

Tawagar MDD ta kammala ziyara a kasashen Sahel

Manzannin Majalisar Dinkin Duniya a yankin Sahel lokacin da suka isa Ouagadougou Burkina Faso
Manzannin Majalisar Dinkin Duniya a yankin Sahel lokacin da suka isa Ouagadougou Burkina Faso © Ahmed OUOBA / AFP

Jakadun Majalisar Dinkin Duniya sun kammala ziyarar aiki a yankin Sahel, a kokarin ganin an kafa rundunar wanzar da tsaro da fada da ayyukan tsagerenci a yankin wanda ya kunshi kasashe biyar.

Talla

Jakadan Faransa a Majalisar Dinkin Duniya wanda ke  kuma cikin wannan tawaga Francois Delattre, ya bayyana wa manema labarai a birnin Ouagadougou na Burkina Faso cewa, ya ce wannan rangadi ya ba su damar ganawa da shugabannin kasashen yankin dangane da muhimmancin gaggauta kafa wannan runduna.

Kasashen Burkina Faso, Chadi, Mali, Mauritaniya da kuma Nijar sun yanke shawarar kafa wannan runduna mai suna G5-Sahel ne domin tabbatar da tsaro a yankunan iyakokinsu da yanzu haka ke fama da ayyukan ta’addanci.

Rundunar za ta kunshi dakaru dubu biyar, to sai dai ana bukatar kudi Euro milyan 224 domin daukar dawainiyarta, kudaden da har yanzu bayanai ke cewa an gagara samar da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.