Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun Abuja ta aikawa Jonathan sammace

Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan
Tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan REUTERS/Denis Balibouse
Zubin rubutu: Bashir Ibrahim Idris | Awwal Ahmad Janyau
1 Minti

Wata Kotun Abuja a Najeriya ta bukaci tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan da ya gurfana a gabanta domin bada shaida kan shari’ar da ake yi wa tsohon kakakin Jam’iyyar PDP Oliseh Metuh na karbar kudi sama da miliyan 400 daga hannun Kanal Sambo Dasuki tsohon mai ba shugaban shawara kan sha’anin tsaro.

Talla

Alkali Obang Okon ya ce rashin kiran shugaban domin bayar da bahasi kamar yadda Metuh ya bukata ba zai yi wa wanda ake zargi adalci ba.

Alkali Okon ya ce wannan ne ya sa dole a gare shi ya sanya hannu wajen ganin tsohon shugaban ya gurfana a gaban kotun domin bada shaida kan wadannan makudan kudaden.

Metuh ya shaidawa kotun cewa da amincewar Jonathan ya karbi makudaden kudaden daga hannun Sambo Dasuki. Akan haka ne kotun ke ta bukaci Jonathan ya gurfana gabanta domin bayar da shaida.

Haka kuma kotun ta amince da bukatar da lauyoyin da ke kare Mista Metuh suka shigar kan ganin Dasuki ya gurfana domin bayar da shaida a gaban kotun.

Sambo Dasuki da ake tsare da shi tun a 2015 yana fuskantar shari’a ta daban kan zargin sama da fadi da sama dala biliyan biyu da aka ware domin sayo makaman yaki da Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.