Kenya

'Yan adawar Kenya za su kauracewa zabe

Jagoran adawar Kenya Raila Odinga.
Jagoran adawar Kenya Raila Odinga. REUTERS/Baz Ratner

Hukumar zaben Kenya ta ce zaben shugabancin kasar da za a sake a gobe Alhamis zai gudana kamar yadda aka tsara, duk da zaman dar-dar din da ake ciki a kasar. Tabbacin Shugaban hukumar zaben Wafula Chebukati, ya zo ne bayan da, kotun kolin kasar ta gaza sauraron karar dakatar da zaben, saboda rashin bayyanar manyan alkalanta 5.

Talla

A jiya Talata ne dai wasu ‘yan bindiga suka hallaka wani mai tsaron lafiyar, daya daga cikin alkalan 7 da ya kamata su halarci zaman kotun kolin na yau, don sauraron bukatar dakatar da zaben na gobe.

Yayin bada tabbacin kin janye zaben, shugaban hukumar zaben ta Kenya, Wafula Chebukati ya ce tuni jami’an tsaron kasar suka bada tabbacin kare lafiyar ma’aikatansa dan haka babu gudu ba ja da baya.

Sai dai kuma za a iya cewa tsugunno bata kare ba, domin kuwa ba da dadewa ba ne jagoran adawar kasar Raila Odinga ya bukaci kafatanin magoya bayansa su kauracewa zaben na gobe.

Ana dai ganin matakin na Odinga ya zo sakamakon alwashin da wasu gungun magoya bayansa su ka sha na cewa ba za su bari zaben ya gudana a yankin Kisumu da ke yammacin kasar ta Kenya ba, wato yankin da suke da rinjaye.

Alwashin dai ya jefa tsoro a zukatan ma’aikatan hukumar zaben kasar, kasancewar a halin da ake ciki, jami’ai 5 kadai suka isa yankin daga cikin 400 da ya kamata su hallara, kamar yadda baturen zaben yankin John Ngutai ya tabbatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.