ECOWAS

Za a dauki lokaci kafin samar da kudin bai-daya na ECOWAS

Ba za a iya samar da kudin bai-daya ba na kasashen ECOWAS zuwa 2020
Ba za a iya samar da kudin bai-daya ba na kasashen ECOWAS zuwa 2020 femi adeshina facebook

Taron shugabannin kasashen Yammacin Afirka kan samar da takardar kudin bai-daya a yankin wanda aka gudanar a birnin Yamai, ya jaddada goyon bayansa ga manufar, amma ba za a iya soma amfani da tsarin a shekara ta 2020 mai zuwa kamar yadda aka yi hasashe ba.

Talla

Shugaban Hukumar Kungiyar ta ECOWAS Marcel de Souza, wanda ke gabatar da jawabi a wurin taron, ya ce akwai manyan manufofi hudu da ya kamata a cimma kafin samar da takardar kudin na bai-daya.

Kwamitin tattauna batun kudin na bai-daya ya kunshi shugabannin Nijar da Ghana da Najeriya da Togo
Kwamitin tattauna batun kudin na bai-daya ya kunshi shugabannin Nijar da Ghana da Najeriya da Togo Femi Adesina Facebook

Manufofin sun hada da gazawa wajen daidaita kudin da mambobin ECOWAS ke amfani da su da kuma tabbatar da tsarin kudi da zai bada damar kafa babban bankin da zai tafiyar da kudin na bai-daya.

A cewarsa har zuwa yanzu babu daya daga cikin manufofin da aka cimma.

An yi Taron samar da kudin ECOWAS a Nijar

Manufar taron da aka gudanar a Yamai shi ne dibawa tare da nazari akan ci gaban da aka samu ga kudirin samar da kudin na bai-daya a cikin shekaru 30.

A 2014 ECOWAS ta nada kwamitin shugabannin kasashen da za su tattauna batun bayan daura alhakin samar da kudin na bai-daya akan Nijar da Ghana.

Kasashen renon Faransa da suka hada da Benin da Burkina Faso da Guinea-Bissau da Cote d’Ivoire da Mali da Niger da Senegal da Togo na amfani ne da kudin bai-daya na CFA.

Amma sauran kasashen mambobin ECOWAS guda 7 na amfani ne da kudinsu, kuma a tsakaninsu babu wanda ya nuna alamun zai iya canzawa.

Shugabannin kasashen yankin biyar ne suka halarci taron karo na hudu da aka gudanar a Yamai, da suka hada da na Cote d’Ivoire da Ghana da Najeriya da Togo da kuma Nijar mai masaukin baki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.