Afrika

Afrika na bukatar kwararru milyan 11 don kaucewa shiga kangin talauci

Wasu daruruwan mutane a gabar teku da ke birnin Durban na kasar Afrika ta Kudu.
Wasu daruruwan mutane a gabar teku da ke birnin Durban na kasar Afrika ta Kudu. REUTERS/Rogan Ward/Files

Majalisar dinkin duniya ta ce nahiyar Africa tana bukatar sama da likitoci, ma’aikatan jiyya da kuma malaman makaranta miliyan 11 nan da shekara ta 2030, domin saita tattalin arziki da tsarin zamantakewar al’umma, don kaucewa kwarar bakin haure daga Afrika zuwa Turai.

Talla

Majalisar ta ce nahiyar Afrika na bukatar miliyoyin kwararrun domin fuskantar kalubalen karuwar yawan yara kanana a nahiyar zuwa miliyan 750 nan da shekaru 13 masu zuwa.

Wani hasashen hukumar UNICEF, ya nuna cewa a karshen karnin da muke ciki, zai zamanto cewa kowane yaro daya cikin biyu da ke rayuwa a fadin duniya, zai kasance ne daga nahiyar Afrika.

Zalika wani binciken da hukumar ta gudanar ya nuna cewa sama da yaro 1 cikin 5 da suka kai shekaru 6 zuwa 11 basa halaratar makaranta.

Majalisar dinkin Duniya ta ce cikin mutane 10 a nahiyar Afrika, akalla 6 ne basa amfana da samun cikakkiyar tsafta, yayinda kuma kashi 1.7 na kwararrun jami’an lafiya ne ke lura da mutane akalla dubu 1 a nahiyar Afrika, sabanin yadda hukumar kula da lafiya ta duniya WHO ta sanya kai’dar kashi 4.45 na kwarrun ne ya kamata su lura da waccan adadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.