Kenya

Hukumar zaben Kenya ta dage kada kuri'a a wasu yankuna

Jagoran 'yan adawa Raila Odinga, yayin shirin jawabi ga magoya bayansa a birnin Nairobi. Ranar 25 ga Oktoba,  2017.
Jagoran 'yan adawa Raila Odinga, yayin shirin jawabi ga magoya bayansa a birnin Nairobi. Ranar 25 ga Oktoba, 2017. REUTERS/Siegfried Modola

Hukumar shirya zaben Kenya, ta dage shirin kada kuri’u da yakamata a yi yau Asabar, a wasu yankunan da ‘yan adawa ke da rinjaye.

Talla

Hukumar ta ce, ta dauki matakin ne, don kaucewa sake samun zubda jini sakamakon arrangama tsakanin ‘yan adawar da jami’an tsaron kasar, zalika domin kare lafiyar jami’anta.

Rundunar ‘yan sandan kasar ta ce, akalla mutane 6 suka rasa rayukansu a dalilin rikici kan zaben shugabancin kasar da kotun koli ta bada umarnin sake wa, bayan soke na farko da shugaba mai ci Uhuru Kenyatta yayi nasara.

Jim kadan da fara kada kuri'u a zaben da aka fara a ranar Alhamis  da ta gabata, aka fara samun arrangama tsakanin jami’an tsaro da magoya bayan jagoran ‘yan adawa Raila Odinga.

Karo na biyu kenan ana dage zaben a wasu manyan yankunan kasar guda hudu, lamarin da yasa ake zaman dar-dar, bayan kauracewa zaben da Odinga hadi da magoya bayansa suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.