Burkina Faso

An cakfe kanen tsohon shugaba Compaore a Faransa

François Compaoré, kanen tsohon shugaban Burkina Faso Blaise Compaoré.
François Compaoré, kanen tsohon shugaban Burkina Faso Blaise Compaoré. © AFP PHOTO / Ahmed OUOBA

An cafke Francois Compaore, kanen tsohon shugaban Burkina Faso a birnin Paris na Faransa a karkashin wani sammacin kasa da kasa bisa zargin sa da hannu wajen kisan wani shahrarren dan jaridar Burkina Faso Norbert Zongo a 1998.

Talla

An cafke Compaore ne a lokacin da ya sauka filin jiragen saman Charles-Gaulle kamar dai yadda lauyan da ke kare shi ya tabbatar.

François Compaoré, ya jima yana ziyartar Faransa inda matarsa ke zaune ba tare da ya fuskanci wata matsala ba sai a jiya lahadi, yayin da gwamnatin Burkina Faso ke neman a taso ma ta keyarsa domin ya fuskanci shara’a gida.

Lauyan da ke kare iyalan marigayi Norbert Zongo Me Benewende Sankara, ya bayyana farin cikinsa da wannan kame, inda ya ce zai share fage domin gano gaskiya dangane da zargin da ake yi wa kanen tsohon shugaban kasar Blaise Compaore da ke gudun hijira a Cote d’Ivoire wajen kashe dan jaridar da kuma sauran masu hamayya da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.