Nijar

An raunata 'yan sanda 23 da kona motoci 14 a tarzomar Yamai

Bazoum Mohamed Ministan cikin gidan Nijar
Bazoum Mohamed Ministan cikin gidan Nijar

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce ‘yan sanda 23 ne suka samu raunuka a aragamar da suka yi da masu zanga-zangar adawa da daftarin dokar kasafin kudin kasar na shekara ta 2018 da aka yi jiya lahadi a birnin Yamai.

Talla

Ministan cikin gidan kasar Bazoum Mohamed, ya ce 4 daga cikin ‘yan sandan sun samu munanan raunuka, yayin da aka kona ko lalata motoci 14 cikin har da 10 na jami’an tsaro.

A lokacin tarzomar wadda kungiyoyin fararen hula suka kira, masu zanga-zangar sun kona ofishin ‘yan sanda da ke babbar kasuwar Yamai tare da farfasa wani bangare na ginin hukumar zaben kasar wato CENI.

Ministan cikin gida Bazoum Mohamed ya zargin magoya bayan jam’iyyar adawa ta MODEN ta Hama Amadou da ke gudun hijira a waje da hannu waje da ke kokarin yin amfani da wannan dama domin shirya tarzama makamanciyar wadda aka yi a Burkina Faso domin kifar da gwamnati.

Ministan ya ce duk wanda aka sama da laifi a wannan tarzoma za a hukuntar da shi kamar yadda dokokin kasar suka shata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.