Kamaru

Kotun Kamaru ta daure wani dan adawa shekaru 25

shugaban kasar Kamaru  Paul Biya a zauren taro  Majalisar Dinkin Duniya karo  na 71.
shugaban kasar Kamaru Paul Biya a zauren taro Majalisar Dinkin Duniya karo na 71. REUTERS/Mike Segar

Wata Kotun soji a kasar Kamaru ta zartar da daurin shekaru 25 na zama gidan yari ga wani shugaban 'yan adawar kasar Aboubakar Siddique, saboda zargin sa da aikata laifin cin amanar kasa, tare kuma da kokarin jefa kasar cikin rikici.

Talla

Siddique na jagorantar daya daga cikin Jam’iyyun adawa a Yankin Arewacin kasar ta Kamaru ne. Lauyan sa Emmanuel Simh ya ce, za su daukaka kara, a ya yin da kungiyar Amnesty International ta bayyana hukuncin a matsayin yunkurin murkushe Yan adawa.

Gwamnatin kasar Kamaru dai ta yi kaurin suna a tsakankanin kungiyoyin kare hakkin ‘yan adam na duniya dake zarginta da keta hakkin dan adam ta hanyar mulkin kama karya na sama da shekaru 40 da shugaba Paul Biya ya assasasa a kasar dake yankin tsakkiyar Afrika, da kuma ke fama da rikicin Boko Haram da yanzu ke ci gaba da lakume rayukan fararen hula a yankin, dake makwabtaka da tarayyar Nigeria.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.