Jamhuriyar Congo

"Rikicin Jamhuriyar Congo ya raba mutane rabin miliyan da gidajensu"

Masu adawa da shugabancin Joseph Kabila, yayinda suke zanga-zangar neman tilasta masa sauka daga shugabanci, bayan karewar wa'adinsa.
Masu adawa da shugabancin Joseph Kabila, yayinda suke zanga-zangar neman tilasta masa sauka daga shugabanci, bayan karewar wa'adinsa. REUTERS/Kenny Katombe/File Photo

Wata kungiyar lura da ‘yan gudun hijira ta kasar Norway, NRC, ta ce sama da al’ummar Jamhuriyar Demokradiyar Congo rabin miliyan sun tsere daga rikicin kabilanci a kudu maso gabashin kasar, tare da gargadin cewa kin daukar matakan gaggawa na iya jefa yankin cikin mummunan bala’i.

Talla

Shekaru 4 aka shafe ana samun tashin hankali tsakanin mayakan Luba na kabilar Bantu, da Twa da ke lardin Tanganyika, rikicin da ya haddasa rasa rayukan daruruwan mutane, tare da tursasawa dubbai gudun hijira a Zambia da ke makwabtaka da kasar.

Rikicin da ya sake tsananta a watannin baya-baya nan, na daga cikin munanan matsalolin jin-kai da ake fuskanta a Congo.

Karuwar rashin zaman lafiya tsakanin mayakan masu hamayya da juna, da kuma turjiya da shugaba Joseph Kabila ke nunawa na kin sauka daga mulki duk da cikar wa’adinsa a watan Disamba na bara, na daga cikin manyan dalilan da ke barazanar tsoma kasar ta Jamhuriyar Congo cikin munin yanayi.

A watan da ya gabata, Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana kasar ta Congo cikin jerin kasahen duniya da ke da bukatar agajin gaggawa bayan Iraqi, Syria da kuma Yemen, inda al’ummar kasar miliyan 4 suka rasa matsugunai.

Zalika hukumar lura da 'yan gudun hijirar ta kasar Norway, NRC, ta ce sama da kashi 80 cikin 100 mutane kasar da ke rayuwa a sansanin ‘yan gudun hijira basa samun ruwan sha mai tsafta.

Zalika akwai yara kusan dubu 600 da ke fuskantar hadarin yunwa yanzu haka a yankin Kasai, inda mutane dubu biyar suka rasa rayukansu saboda rashin zaman lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI