Sudan ta Kudu

Sudan ta Kudu ta haramta kafa kungiyoyin 'Yan Jaridu

Hoton shafin farko na jaridar New Times mai zaman kanta da ke kasar Sudan ta Kudu.
Hoton shafin farko na jaridar New Times mai zaman kanta da ke kasar Sudan ta Kudu. RFI

Gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ta haramta kafa kungiyoyin ‘yan jaridu, tare kuma da daukar matakin tilasta ganin dukkan kafofin yada labarai a kasar sun sabunta lasisin ayyukansu cikin mako daya.

Talla

Matakin ya sanya kungiyoyin fararen hula da kuma ‘yan jaridu da ke kasar fargabar cewa, matakin na gwamnatin Sudan ta Kudu, yunkuri ne na sanya wa aikin jarida takunkumi na din-din a kasar

Babu wasu bayanai daga jami’an ma’aikatar yada labaran kasar ko kuma hukumar sadarwa, game da wannan sabuwar doka.

Wasu kungiyoyin aikin Jarida da kuma kungiyoyin kare hakkin dan adam, sun shaidawa kamfanin Dillancin labaran Reuters cewa matakin, yunkuri ne kawai na muzgunawa kafofin yada labarai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.