Kamaru

Kungiyar dake kare hakkokin Yan Jaridu ta duniya zata karrama Ahmed Abba

Ahmed Abba wakilin sashen hausa na rediyon Faransa dake tsare a Kamaru
Ahmed Abba wakilin sashen hausa na rediyon Faransa dake tsare a Kamaru

Kungiyar dake kare hakkokin Yan Jaridu ta duniya zata karrama wasu fitatun Yan Jaridu 4 saboda gwagwarmayar da suka yi wajen gudanar da aikin su da kuma irin azabtarwar da suke fuskanta, cikin su harda Ahmed Abba, wakilin Sashen Hausa na RFI.

Talla

Sauran yan jaridu sun hada da Patricia Mayorga ta Mexico da Pravit Rojanaphruk na Thailand da Afrah Nasser na kasar Yemen.

Sanarwar da kungiyar ta bayar ya bayyana cewar za’ayi bikin ne a Amurka, ranar 15 ga watan nan a karkashin jagorancin Christine Amanpour ta CNN.

Ita kuwa Patricia Mayorga, wakiliyar mujallar Proceso a Mexico, ta shiga wannan sahun ne bayan barazanar kisa da aka yi ma ta sakamaon rahotonta kan alakar Jam’iyyar kasar mai mulki da kuma miyagun ayyuka da suka hada da satan jama’a har ma da cin zarafin fararen hula.

Shi kuwa Pravit Rojanaphruk na Thailand ya samu wannan karramawar ce bayan gwamnatin kasar ta ci mutuncinsa tare daure shi har sau biyu saboda rahotanninsa kan siyasa da kuma kare hakkin bil-adama.

Sai kuma Afrah Naseer, fitacciyar ‘yar jarida a Yemen, wadda aka tirsasa ma ta neman mafaka a Sweden bayan an yi barazanar daukan ranta saboda rahotanninta kan keta hakkin dan adam da cin zarafin mata da kuma dakile ‘yancin ‘yan jaridu da gwamnatin kasar ke yi.

Daraktan kungiyar Joel Smith ya ce ana bada irin wannan kyauta ne ga ‘yan jaridun da suka fuskanci barazanar kisa ko dauri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.