Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Congo

Rikicin Congo: An hallaka mutane 7 a birnin Bukavu

Wasu daga cikin dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya da ke Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.
Wasu daga cikin dakarun wanzar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya da ke Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo. cfr.org
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Rundunar sojin Jamhuriyar Congo ta ce mutane 7 sun rasa rayukansu sakamakon fadan da aka gwabza tsakanin sojin gwamnati, da wasu mabiya tsohon Hafsan sojin kasar da aka kora a garin Bukavu.

Talla

Daga bisani majiyar sojin jamhuriyar Congo ta ce, Kanal Abbas Kayonga ya mika kansa ga rundunar sojin wanzar da zaman lafiya ta majalisar dinkin duniya.

Kakakin rundunar sojin kasar da ke shiyyar kudancin yankin Kivu Dieudonne Kasereka, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na reuters cewa, kazamin gadan ya barke ne a lokacinda ‘yan sanda suka je gidan Kanal Abbas Kayonga da nufin karbe makaman da ke karkashinsa, bayan korarsa daga rundunar sojin kasar a ranar Alhamis da ta gabata.

Kanal kayonga ya taba kasancewa mayakin wata kungiyar ‘yan tawaye, da ta ajiye makamai kuma aka shigar da ita cikin rundunar sojin Jamhuriyar Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.