Mali

Jiragen yakin Faransa sun hallaka Sojin Mali da ke hannun mayakan jihadi.

Kawo yanzu dai ma'aikatar tsaron Mali ta ki bayyana adadin bannar da harin ta sama karkashin jagorancin Fransa ya haifar, haka zalika bata bayyana adadin sojin da suka mutu ba.
Kawo yanzu dai ma'aikatar tsaron Mali ta ki bayyana adadin bannar da harin ta sama karkashin jagorancin Fransa ya haifar, haka zalika bata bayyana adadin sojin da suka mutu ba. Reuters

Ma'aikatar tsaron kasar Mali ta ce wani harin sama da jiragen Faransa suka kai kan mayakan Jihadi da ke tada kayar baya a yankin Arewacin kasar yayi sanadiyyar mutuwar wasu sojojin Mali da kungiyar ke garkuwa da su.

Talla

Wata sanarwar da ma’aikatar tsaron ta bayar, ta nuna cewar cikin wadanda suka mutu a harin na Faransa har da sojojin kasar da mayakan suka yi garkuwa da su.

Duk da cewa dai ma'aikatar tsaron ba ta bayyana gaskiyar adadin sojin da suka rasa rayukansu a harin ba, amma kafofin yada labaran Mali sun ce akalla sojoji 11 ne suka mutu.

Kakakin sojin Faransa, Kanar Patrick Steiger ya ce Mali ce ke da hurumin bayar da bayani akan abinda ya faru a kasar ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.