Chadi

Komi ya tsaya cik a kotunan Chadi

Idriss Déby, Shugaban kasar Chadi
Idriss Déby, Shugaban kasar Chadi REUTERS/Alain Jocard/Pool

Yau kwanaki 11 kenan da alkalai ke gudanar da yajin aiki a kasar Chadi, lamarin da ya sa ayyuka suka tsaya cik a cikin kotunan kasar.Malaman shari’ar sun bukaci a biya su kudaden alawus sakamakon ayyukan da suka yi a bara

Talla

Alkalan na yajin aiki ne domin neman a biya su wasu kudade na alawus, da kuma biyan wasu makuddan kudade da gwamnatin kasar ta yanke wa ma’aikatan shara’a a karkashin matakin tsuke bakin aljihun gwamnati a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.