Najeriya

Yan Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya

Mayakan Boko Haram
Mayakan Boko Haram REUTERS/Zanah Mustapha

Akala Dakarun Najeriya uku ne suka rasu a wani harin kwantar bauna da yan kungiyar Boko Haram suka yiwa sojojin Najeriya a daf da dajin Sambisa.

Talla

Mayakan Boko Haram su kaiwa sojojin Najeriya hari ne a lokacin da Dakarun Najeriya dake aiki a yankin suka kama hanyar komawa Gwoza.

A cewar daya daga cikin kato da gora mai suna Harouna Tola yan Boko Haram dauke da manyan makamai sun gewaye sojojin Najeriya cikin dan karamin lokaci,tareda bude masu huta ba kakautawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.