Burundi

Kasashen gabashin Afrika sun zargi ICC da yi musu katsalandan

Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni a (bangaren hagu) tare magatakardan kungiyar kasashen gabashin Afrika, Juma Mwapachu (a tsakiya), yayinda suke rattaba hannu kan takardar bayan taron da suka yi a Arusha. 30 ga watan Nuwamba, 2006.
Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni a (bangaren hagu) tare magatakardan kungiyar kasashen gabashin Afrika, Juma Mwapachu (a tsakiya), yayinda suke rattaba hannu kan takardar bayan taron da suka yi a Arusha. 30 ga watan Nuwamba, 2006. REUTERS/Thomas Mukoya/Files

Gwamnatocin kasashen Uganda da Tanzania, sun yi alla wadai da matakin, kaddamar da bincike kan zargin gwamnatin Burundi da aikata laifukan yaki da kotun kasa da kasa ICC ta yi, inda suka ce hakan zai iya jefa kasar, dama yankin gabashin nahiyar Afrika cikin sabon rikici.

Talla

Shugaban Uganda Yuweri Museveni ya fara tur da matakin a lokacin da ya karbi bakuncin takwaransa John Magfuli na Tanzania.

A ranar Alhamis da ta gabata, kotun ta ICC, ta bada umarnin kaddamar da bincike daga watan Afrilun 2015 zuwa Oktoban 2017, kan zargin da ake yi wa jami’an tsaron Burundi, na kisan sama da mutane 1000, da raba wasu sama da dubu 400,000 da gidajensu, a kokarin murkushe zanga zangar da ‘yan adawar kasar suka shirya kan zarcewa karo na uku da Pierre Nkrunziza yayi a Zaben shugabancin kasar, zaben da ‘yan dawa suka ce ya haramta a gareshi.

Shugaban Uganda Yuweri Museveni, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar kasashen gabashin nahiyar Afrika EAC, ya zargi kotun ICC da yin katsalandan cikin al’amuran da suka shafi kasashen, ba tare da ta shawarce su ba.

Kasashen gabashin nahiyar Afrika da ke karkashin kungiyar ta EAC, sun hada da Uganda, Tanzania, Kenya, Burundi, Rwanda, da kuma Sudan ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.