Benin

Likitoci na ci gaba da yajin aiki a Jamhuriyar Benin

Masu zanga-zangar lumana a Jamhuriyar Benin
Masu zanga-zangar lumana a Jamhuriyar Benin Delphine Bousquet/RFI

Shugaban Jamhuriyar Benin Patrice Talon ya gana da shugabanin kungiyoyin kwadago bangaren kiwon lafiya, wata hanyar samu masalha dangane da yajin aiki da bangaren kiwon lafiya na kasar ya samu kan sa tun a watan Agusta na wannan shekara.

Talla

Shugaban ya bayyana bacin ran sa, tareda yi kira zuwa ma’aikantan kiwon lafiya da cewa su yiwa Allah su koma aikin su.

Wakilan ma’aikantan kiwon lafiya sun jaddadawa shugaban kasar ta Benin cewa hanyar kawo karshen yajin shine Gwamnatin ta samar da hanyoyin na kyautata rayuwar su,wanda yi haka zai inganta sashen kiwon don ceto rayukan jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.