Najeriya

Wani Soja ya harbe karamin hafsa a Borno

Dakarun Najeriya  a jihar Borno
Dakarun Najeriya a jihar Borno Photo: Stefan Heunis

Rundunar Sojin Najeriya ta kaddamar da bincike domin gano dalilin da ya sa wani soja ya harbe wani karamin hafsa mai mukamin Kaftin kafin daga bisani ya hallaka kan sa a Chibok dake jihar Borno.

Talla

Daraktan yadda labaran rundunar Janar Sani Usman Kuka sheka ya bayyana cewar, Kaftin din ya samu labarin cewar, wani mai rike da mukamin ‘Staff Sajen’ ya dirki barasa ne kuma yana aikata wasu halaye da suka saba ka’idar aiki, abinda ya sa ya ruga domin dawo da shi sansanin su.

Yayin da ake kokarin karbe makamin sa ne, Sajen ya harbe Kaftin tareda wasu sojojin hudu kana ya hallaka kan sa.

Yanzu dai haka an kai gawarwakin jami’an biyu asibitin Yola.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.