Zimbabwe

Sojojin Zimbabwe sun tsare Mugabe da iyalansa

Wasu motocin sulke na sojojin kasar Zimbabwe, yayin da suka kutsa tare da mamaye wasu titunan babban birnin kasar Harare. 14 ga Nuwamba, 2017.
Wasu motocin sulke na sojojin kasar Zimbabwe, yayin da suka kutsa tare da mamaye wasu titunan babban birnin kasar Harare. 14 ga Nuwamba, 2017. REUTERS/Philimon Bulawayo

Rahotanni daga kasar Zimbabwe sun ce sojojin kasar suna tsare da shugaban kasa Robert Mugabe tare da iyalansa, jim kadan bayan da rundunar sojin ta kwace iko da hedikwatar gidan Talabijin na kasar tare da tsare dukkan hanyoyin da ke kaiwa ga manyan ofisoshin ma’aikatun gwamnati da kuma majalisa da ke birnin Harare.

Talla

Rahotanni sun ce an ji karar musayar wuta a wasu sassan birnin, cikin harda kusa da gidan shugaba Robert Mugabe, wanda daga bisani jam'iyyar ZANU PF, ta tabbatar da cewa, an samu musayar wutar ce tsakanin wasu jami'an gwamnatin Mugabe da suke yi kokarin turjewa kamun da sojoji za su yi musu.

Sai dai a baya, cikin wani jawabi da ya gabatar ta kafar Talabijin da safiyar yau, kakakin rundunar sojin kasar, Manjo Janar SB Moyo, ya musanta cewa sojojin sun kutsa cikin birnin Harare ne domin yi wa shugaban kasar Robert Mugabe juyin mulki.

Manjo Janar Moyo ya ce shugaban kasa Mugabe tare da iyalansa suna cikin koshin lafiya, kuma babu wata barazana ga rayuwarsu.

A cewar kakakin, sojojin suna kai hari ne kan wasu masu aikata laifuka a kusa da shugaban kasar, wadanda suke haifar da matsaloli ga jin dadin rayuwa da kuma tattalin arziki domin ganin an hukunta su.

Tun a ranar Litinin babban hafsan sojin kasar Janar Constantino Chiwenga, yayi jawabin cewa ba zasu bari a cigaba da korar wadanda suka taka rawa wajen samun ‘yancin kan kasar ba.

Chiwenga ya yi barazanar cewa sojoji za su iya fadawa a fagen siyasar kasar, bayan da Robert Mugabe ya tube mataimakinsa Emmerson Mnangagwa daga mukaminsa, matakin da ake kallo a matsayin share wa matarsa Grace Mugabe fage, domin darewa kan karagar shugabancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.