Bakonmu a Yau

Bashir Ibrahim Idris kan murabus din Robert Mugabe

Sauti 03:19
Daruruwan 'yan kasar Zimbabwe, a birnin Harare, yayin da suke murnar saukar Robert Mugabe daga shugabanci.
Daruruwan 'yan kasar Zimbabwe, a birnin Harare, yayin da suke murnar saukar Robert Mugabe daga shugabanci. REUTERS/Mike Hutchings

Dubban ‘yan kasar Zimbabwe sun barke da kade-kade da bushe-bushe, bayan samun tabbacin Robert Mugabe ya sauka daga shugabancin kasar. Kakakin majalisar kasar Jacob Mudenda ne ya bada tabbacin murabus din na Mugabe, a cikin wasika da ya aikewa majalisar kasar a yau Talata, yayinda suke tsaka da muhawara, kan aiwatar da kudirin tsige shi. Umayma Sani AbdulMumin ta tattauna da Bashir Ibrahim Idris kan halin da siyasar Zimbabwe ke ciki da kuma yanayin da ya dabaibaye murabus din Robert Mugabe.