Chadi

Chadi ta karyata zargin cin hanci da ake yi wa Deby

Shugaban kasar Chadi Idriss Déby.
Shugaban kasar Chadi Idriss Déby. Ludovic MARIN / AFP

Gwamnatin kasar Chadi ta yi watsi da zargin cin hanci da Amurka ta yi wa shugaba Idris Deby na karbar Dala miliyan 2 domin bai wa wani kamfanin hakar man China izinin gudanar da aiki a kasar.

Talla

Gwamnatin ta bayyana damuwa a kan yunkurin bata wa shugaban kasa Deby suna.

Kasar Amurka ta gurfanar da tsohon Ministan cikin gidan Hong Kong, Chi Ping Patrick Ho da tsohon ministan harkokin wajen Senegal Cheikh Gadio da ake zargi da taimakawa wajen mika cin hancin ga jami’an kasashen Chadi da Uganda a gaban kotu.

Ma’aikatar shari’ar Amurka ta ce Ho ya aike wa Gadio da Dala 400,000 domin bai wa shugaba Idris Deby a madadin wani kamfanin makamashi da ke kasar China.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI