Najeriya

Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar APC

Atiku Abubakar  Tsohon mataimakin shugaban Najeriya
Atiku Abubakar Tsohon mataimakin shugaban Najeriya AFP/PIUS UTOMI EKPEI

Tsohon Mataimakain Shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya sanar da janyewar sa daga Jam’iyyar APC mai mulkin kasar a wata wasika da ya rubuta mata ya kuma rabawa manema labarai.

Talla

Wasikar ta bayyana cewar, Atiku ya amsa kiran dimbin mutane na shiga Jam’iyyar APC a shekarar 2013 da fatan cewar za’a samu ci gaban dimokiradiya da adalci ga kowa da kuma gina kasa, amma hakan bai samu ba.

Tsohon mataimakin shugaban ya kawo misali kan wasikar da wani Gwamna ya rubutawa shugaban kasa wadda ke tseguntawa manema labarai kan tabarbarewar al’amura a Jam’iyyar da kuma shugabancin kasar, amma kuma har ya zuwa yanzu babu wanda yace komai, kuma babu abunda ya sauya.

Atiku ya ce wasikar Gwamnan ta kuma yi nuni kan rashin jituwa da tintubar wasu jiga jigan Jam’iyyar kan halin da ake ciki da suka hada da Bola Ahmed Tinubu da Atiku Abubakar da Rabiu Musa Kwankwaso amma babu abinda ya sauya.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce, bayan ganawa da Ubangijin sa da iyalan sa da magoya bayan sa da kuma mutanen Najeriya daga sassa daban daban ya dauki aniyar janyewa daga cikin Jam’iyyar ta APC domin nazari kan makomar sa nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.