Afrika ta Kudu

Oscar Pistorious zai shafe shekaru 15 a gidan yari

Tsohon shahararren dan wasan gasar Olympics na kasar Africa ta Kudu Oscar Pistorius a lokacin da wata kotun kasar ke sauraron shari'ar zargin da ake masa na kashe budurwarsa Reeva.
Tsohon shahararren dan wasan gasar Olympics na kasar Africa ta Kudu Oscar Pistorius a lokacin da wata kotun kasar ke sauraron shari'ar zargin da ake masa na kashe budurwarsa Reeva. REUTERS/Kim Ludbrook/Pool/File Photo

Wata kotun kasar Afrika ta Kudu, ta kara yawan shekarun da shahararren mai wasannin motsa jiki Oscar Pistorious zai shafe garkame a gidan yari, sakamakon samunsa da laifin hallaka budurwarsa da bindiga.

Talla

Da fari wata kotu ta yanke wa Pistorious hukuncin shekaru 6 ne bisa lafin kashe budurwar tasa Reeva Steenkamp, kafin daga bisani masu gabatar da kara, su yi nasara a daukaka karar da suka yi na neman a kara yawan shekarun da dan wasan Olympics din zai yi a gidan yari zuwa shekaru 15.

A ranar Masoya da ake yi wa lakabi da Valentine, ta shekarar 2013, Pitorious ya harbe Reeva, sai dai a cewarsa yayi hakan ne a rashin sani, domin yayi zaton barawo ne ya shigo masa gida.

Bincike ya nuna sau 4 Pistorious yana harbin budurwarsa Reeva, ta jikin kofar bandakin da ta ke ciki, a gidansu da ke birnin Pretoria.

Sau shida Pistorious ya lashe kyautar Zinare a gasar Olympics da ake shiryawa masu fama da nakasa, kasancewar an yanke masa kafafu daga kan gwiwarsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.