Olympio ya bukaci Shugaban Togo ya sauka daga karagar mulkin kasar
Wallafawa ranar:
Shugaban Togo Faure Gnassingbe ya kai ziyara zuwa garin Sokode a wani shirin sa na kwantarwa yan kasar da hankula, a wani lokaci da wasu yan adawa suka bukaci ya sauka daga shugabancin kasar.
Shugaba Faure ya bayyana fatar sa na ganin an kawo karshen tankiyar da ke hana ruwa guda tareda zama teburin tattaunawa da masu adawa da shi.
Gilchrist Olympio madugu yan siyasar Togo a yau talata ya shigar da kira zuwa Shugaban kasar Faure Gnassingbe da cewa lokaci ya yi na ya sauka.
Dan adawa Olympio ya bayyana cewa rikicin da kasar ta fuskanta tsawon watanni uku a baya na nuna ta yadda yan kasar ta Togo suka bijerewa Gwamnatin sa.
A cikin watanni biyu akala mutane 16 ne suka rasu,da dama daga cikin masu zanga-zanga ne suka samu rauni, Olympio mai shekaru 80 tareda hadin guiwar wasu jam'iyyun siyasar kasar 14 sun bayyana fatar su tareda bukatar saukar Faure Gnassingbe daga karagar mulkin Togo.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu