Bakonmu a Yau

Ibrahim Yacouba a kan abubuwan da aka tattauna wurin taron AU-EU

Sauti 03:56
Shugabannin kasashen Turai da Afirka da dama ne ke halartar taron AU-EU a Abidjan.
Shugabannin kasashen Turai da Afirka da dama ne ke halartar taron AU-EU a Abidjan. Reuters

A ranar Laraba 29 ga watan Nuwamba, 2017 ne aka fara taron koli karo na biyar da zai hada shugabannin kasashen Turai da na Afrika a birnin Abidjan na kasar Cote d’Ivoire. Wakilai sama da dubu biyar daga kasashe da kuma kungiyoyi akalla 80 ne ke halartar wannan taro da zai mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi matasa a wannan zamani. Abdoulkarim Ibrahim Shikal daga birnin na Abidjan ya zanta da ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijar Ibrahim Yacouba dangane da abubuwan da taron zai mayar da hankali a kai.