Najeriya

Shugaba Buhari zai halarci taro kan yaki da ta'addanci

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na shirye-shiryen kai ziyara Jordan don halartar wani taro kan ta'addanci..
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari na shirye-shiryen kai ziyara Jordan don halartar wani taro kan ta'addanci.. RFIHausa/Kabiru Yusuf

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyarar kasar Jordan tsakanin ranakun 2 zuwa 3 ga watan Disamba mai kamawa domin halartar taron kasashen duniya 48 kan yaki da ta’addanci.

Talla

Mai baiwa shugaban shawara kan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya ce taron na kwanaki biyu da ake saran Sarki Abdallah ya jagoranta, zai samu halartar ministoci da shugabannin hukumomin tsaro da kuma kungiyoyin fararen hula.

Sarki Abdallah na Jordan a watannin baya ya taimakawa Najeriya da jiragen yaki domin yaki da kungiyar boko haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.