Congo Dimokuradiyya

Hari daga yan tawayen ADF ya halaka dakarun Majalisar Dinkin Duniya a DRC

Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a lardin Kivu
Dakarun Majalisar Dinkin Duniya a lardin Kivu Photo MONUSCO/Force

Wasu yan bidinga dauke da manyan makamai sun kai wani kazamin hari zuwa rundunar wanzar da zaman lafiya a Jamhuriyar Dimokuradiyya Congo, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojan wanzar da zaman lafiya 15 dake aiki a kasar.

Talla

Wannan dai ne hari mafi muni da aka taba kaiwa rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya bayan na Somaliya a shekara ta 1993, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar sojan wanzar da zaman lafiya 24 yan kasar Pakistan a Somaliya

Hukumomin kasar dama mai magana da yahu rundunar wanzar da zaman lafiya a kasar na zargin mayyakan kungiyar ADF, hadakar rundunar tabbatar da Dimokuradiyya daga Uganda kuma musulmai dake arewacin Kivu daf da kan iyaka da kasar Uganda.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutters ya yi Allah wadai tareda bukatar gani an gudanar da bicinke a kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI