Kamaru

'Yan tawaye sun kai wa Sojoji hari a Kamaru

Ana fama da tashe-tashen hankula a yankin masu amfani da turancin Ingilishi a Kamaru
Ana fama da tashe-tashen hankula a yankin masu amfani da turancin Ingilishi a Kamaru STRINGER / AFP

Hukumomi tsaron kasar Kamaru sun ce wasu ‘yan bindiga da suka fito daga yankin da ke amfani da yaren Ingilishi masu neman ballewa sun kai hari kan wani kauye tare da farwa jami’an Sojin kasar.

Talla

A cewar hukumomin tsaron cikin daren jiya ne ‘yan bindigar suka farwa kauye da ke samun kulawar sojoji sakamakon ayyukan ta’addanci da ke ta’azzara.

Ko da ya ke babu tabbacin wadanda suka kai harin amma akwai kyakkyawan tsammanin ‘yan bindigar sun fito ne daga yankin da ke amfani da yaren Ingilishi la’akari da yadda su ke kai makamantan hare-haren kan bukatarsu ta ganin an fitar da su daga Kamaru.

Ma’aikatar yada labaran kasar ta ruwaito cewar sun yi awon gaba da manyan bindigogi 26 da kananan bindigu da wayoyin salula 20 sai kuma riguna masu tambarin jami’an tsaron yankin mai amfani da yaren Ingilishi.

Al’ummar yankin kudancin kasar masu amfani da yaren Ingilishi da basu fi kaso 20 cikin dari na kasar mai yawan jama’a milyan 23 ba, sun jima suna zanga-zangar neman ballewa daga kasar ta Kamaru inda kuma shugaba Paul Biya ya yi watsi da bukatar, lamarin da ya sa suka shiga tashe-tashen hankula.

Duk da cewa an sanya dokar ta baci, amma cikin watan Satumba kadai an hallaka kimanin mutum 40, yayinda cikin Nuwamba aka kashe mutum 10 da kuma jami’an tsaro 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI