ECOWAS ta yi barazanar daukar mataki kan Guinea-Bissau

Shugaban kasar Guinea-Bissau José Mário Vaz
Shugaban kasar Guinea-Bissau José Mário Vaz © Sia Kambou, AFP

Kungiyar raya kasashen yammacin Africa, ECOWAS, ta ce zata dauki kwakkwaran matakin ladabtarwa a kan kasar Guinea-Bissau, muddin ta gaza ware ware rikicin siyasarta cikin watanni biyu.

Talla

ECOWAS wadda ta kammala taronta a Abuja, babban birnin Najeriya, ta bayyana bacin rai kan yadda ta ce gwamnatin ta Guinea-Bissau, ta gaza shawo kan rudanin siysasar da ta tsinci kanta a ciki, tun a watan Agustan shekarar 2015.

Rikicin dai ya samo asali ne, bayan da shugaban kasa Jose Mario Vaz ya kori Fira ministan waccan lokacin Domingos Simoes Pereira.

A farkon makon nan shugaba Vaz ya yi tayin sabunta tattaunawar sulhu da ‘yan adawa, sai dai gamayyar jam’iyyun, sun yi fatali da bukatar, hakan ya sa ECOWAS ta bukaci shugabannin Togo da Guinea, wato Faure Gnassingbe da Alpha-Conde, su ci gaba da kokarin sansantawa nan da wa’adin watanni 2 da ta deba wa kasar ta Guinea-Bissau.

Tun bayan da Guinea-Bissau ta samu 'yancin kai daga mulkin mallakar Portugal a shekarar 1974, ta yi fama da yawaitar samun juyin mulki a kasar, sai a wannan karon aka samu tsayayyar gwamnatin farar hula, wadda a halin yanzu sabanin siyasa ke barazana ga dorewar dimokaradiyyar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.