DRC

Ana zargin Jami'an tsaro da hannu a kisan gillar Kasai

Rikicin Kasai a DR Congo ya lakume rayuka 3,300 tare da tilastawa miliyan 1.3 gudun hijira
Rikicin Kasai a DR Congo ya lakume rayuka 3,300 tare da tilastawa miliyan 1.3 gudun hijira AFP/File

Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta International Human Rights Federation ta zargi jami’an tsaron Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da wata kungiyar dake dauke da makamai da kitsa kisan gillar da aka yiwa mutane a Yankin Kasai.

Talla

A Rahotan da ta fitar yau laraba kungiyar kare Hakkin Bil Adama ta International Human Rights Federation, ta bayyana cewar Yankin Kasai na Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo a matsayin wanda ya gamu da daya daga cikin mummunar cin zarafin Bil Adama da duniya ta taba gani a tarihi.

Kungiyar ta zargi kungiyar Bana Mura da kuma jami’an tsaron gwamnatin Congo da aikata laifufukan da ake iya danganta su da na yaki kan 'yan kabilar Luba.

Gwamnatin Joseph Kabila na kallon 'yan kabilar Luba a matsayin masu goyan bayan kungiyar Kamwina Nsapu masu adawa da shugabancin kasar.

Cocin Katolika ya ce mutane sama da 3,300 aka kashe a rikicin, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta gano kaburbura 87 da aka birne dimbin mutanen da aka kashe, kuma a kokarin ta na tantance wadanda aka kashen, ita ma aka kashe mata jami’an ta guda biyu.

Rikicin na Congo na da nasaba da kin saukar shugaba Joseph Kabila daga karagar mulki duk da kawo karshen wa’adin mulkin sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.