Liberia-Turai

Kotu ta bayar da belin Guus Kouwenhoven

Guus Kouwenhoven, dillalen makamai dan kasar Netherlands
Guus Kouwenhoven, dillalen makamai dan kasar Netherlands AFP PHOTO - OTC HO

Kotun Afrika ta Kudu ta bayar da belin wani dillalen makamai dan kasar Netherlands Guus Kouwenhoven, wanda aka yanke wa hukuncin daurin shekaru 10 gidan yari bayan samun sa da laifi a yakin basasarar Liberia da kasar Guinee kama daga shekara ta 1991 zuwa 2001. 

Talla

Kouwenhoven, mai shekaru 75 a duniya, an cafke shi ne farkon wannan wata a gidansa da ke birnin Cap na kasar Afrika ta kudu, bayan da kotun kasar Netherlands ta bukaci a tiso ma ta keyarsa zuwa gida.

Alkalin kotu Vusi Mhlanga ya bukaci ya biya beli na kudi milyan daya na rands, za a ci gaba da tsare shi a kasar ta Afirka ta Kudu, bayan kwace ma sa passport.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI