Kenya

‘Yan sandan Kenya sun kai samame makarantar addini a Mombasa

‘Yan sandan Kenya sun kai samame makarantar addinin Islama a Mombasa
‘Yan sandan Kenya sun kai samame makarantar addinin Islama a Mombasa REUTERS/Joseph Okanga

‘Yan Sanda a kasar Kenya sun kai samame wata makarantar addinin Islama da ke birnin Mombasa inda suka kama malamai biyu da kuma wasu yara 100 inda suka ce zasu kare lafiyar su.

Talla

Jami’an tsaron sun bayyana makarantar a matsayin wani sansanin da yara ke samun horon da ke mayar da su masu tsatsauran ra’ayin da ke mayar da su 'yan ta’adda.

Kakakin 'yan Sanda ya ce sun dade suna sanya ido a Makarantar kafin daukar mataki akai.

Sheikh Hassan Omar, jami’i a Majalisar limaman kasar ya ce cikin 'yan sandan da suka kai samamen harda 'yan kasashen waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI