Kamaru

Kotun Sojin Kamaru ta wanke Wakilin RFI Hausa Ahmed Abba

Wakilin Sashen Hausa na Rediyo France International RFI da ke Kamaru, wanda kotun sojin kasar ta garkame shi kan zargin hannu a kungiyar Boko Haram.
Wakilin Sashen Hausa na Rediyo France International RFI da ke Kamaru, wanda kotun sojin kasar ta garkame shi kan zargin hannu a kungiyar Boko Haram. © RFI

Sashen daukaka kara na kotun sojin Kamaru ya wanke Wakilin sashen hausa na rediyo France International rfi Ahmad Abba daga dukkanin zarge-zargen da ake masa.

Talla

Tun a watan Yulin shekarar 2015 ne, jami'an tsaro suka kama Ahmad Abba a Yankin Maroua da ke arewacin kasar ta Kamaru lokacin da yake tsaka da hada wani rahoto da ya shafi kungiyar Boko Haram.

Bayan gurfanar da Ahmad Abba gaban kotu ne kuma a wancan lokaci aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari kan abin da suka kira zargin hannu a ayyukan ta'addanci.

Sai dai kuma bayan daukaka kara, a Safiyar yau Kotun Sojin da ke zama a Yaounde ta wanke Ahmad Abba tare da rage hukuncin zuwa daurin watanni 24 a gidan yari.

Hukuncin kotun na yau, ya nuna cewa Ahmad Abba wanda ya shafe tsawon watanni 29 a gidan yarin Kamarun ya kammala wa'adin da aka yanke masa.

Kafin yanzu dai kungiyoyin kare hakkin bil'adama da na 'yan jaridu sun yi ta fafutukar ganin an sako dan jaridar, yayinda a bangare guda kuma ya samu girmamawa ta musamman daga kungiyar da ke kare hakkokin 'yan Jaridu ta Duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.