Libya

Majalisar Dinkin Duniya ta fara kwashe bakin-haure daga Libya

Kashin farko na Bakin-Haure da hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta fara kwasowa daga kasar Libya, zuwa birnin Rome na kasar Italiya. 22, Disamba 2017.
Kashin farko na Bakin-Haure da hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta fara kwasowa daga kasar Libya, zuwa birnin Rome na kasar Italiya. 22, Disamba 2017. REUTERS/Alessandro Bianchi

Majalisar Dinkin Duniya, ta fara kwashe bakin-haure na nahiyar Afrika daga sansanonin da ake gana musu azaba a kasar Libya zuwa Italiya.

Talla

Karo na farko kenan da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar, ta fara aikin kwashe bakin-haure kai tsaye, zuwa nahiyar turai.

Jirgin farko na sojojin Italiya kirar C-130 ya sauka ne a kasar dauke da mata 110, da kuma kananan yara, yayinda jirgi na biyu ke dauke da wasu bakin hauren sama da 50.

Dubban bakin-haure ne ke makale a Libya, inda ake tsare da su, a sansanonin kasar tamkar bayi, tare da gana musu azaba, bayan yunkurin da suka yin a ketarwa zuwa nahiyar turai.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR ta yi hasashen cewa, akalla bakin-haure dubu 18,000 ake cigaba da tsarewa a sansanoni daban a Libya, kuma nan da shekara mai kamawa, tana sa ran kwashe bakin-hauren akalla 10,000 daga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.