Italiya

Za a kwashe baƙin-haure 10,000 daga Libya zuwa Turai

Mutane a cibiyar tsare masu son tsallakawa Turai a Gharyan, Libya October 12, 2017.
Mutane a cibiyar tsare masu son tsallakawa Turai a Gharyan, Libya October 12, 2017. REUTERS/Hani Amara

Gwamnatin Italiya ta ce akwai yiwuwar a mayar da mutane kimanin dubu goma da ke maƙale a ƙasar Libya zuwa Turai a cikin shekara ta 2018.

Talla

Wannan dai wani mataki ne na magance matsalar tsarewa da kuma cin zarafin ƴan ƙasashen waje a ƙasar ta Libya.

Ministan cikin gida na ƙasar Italiya Marco Minniti ya ce baƙin za su shiga Turai ne a ƙarƙashin wani shiri na taimakon jin ƙai, ba tare da faɗawa cikin haɗari ba.

Hakan na zuwa ne bayan da a ranar Juma’a aka kwashe wasu daga cikin mutanen da suka maƙale a Libya ɗin zuwa birnin Roma na ƙasar ta Italiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.